Mutuwa Ta Dauki matashin Limami a tsakiyar Sujadar Tahajjud A Zaria.
Legit ng Hausa ta samu labarin rasuwar wani Alaranma mai suna Sani Lawal wanda ya rasu a lokacin da yake ibadar sallar dare a watan Ramadan. Kamar yadda mu ka samu rahoto daga majiyoyi da dama, Sani Lawal ya rasu ne a daidai lokacin sujada, yana limancin sallar tahajjud a ranar Asabar dinnan. Tuni dai aka yi jana’izar marigayin dazu da safe da kimanin karfe 8:00 na safe a unguwarsu da ke Layin MB, Samaru, karamar hukumar Sabon Gari, Kaduna.
Wani Aminin Marigayin yace ya bar masallacin bayan an yi raka’a takwas. sai kurum aka kira shi a waya, aka fada masa ai Liman ya fadi a yayin sujuda. Legit.ng Hausa tuntubi wani abokin marigyain, wanda ya shaida mana wannan labari mara dadi. Malam Anas Mansur ya san Marigayin, kuma ya tabbatar mana da cewa ya rasu ne bayan ya yi sujudar tilawar Al-kur’ani da ke cikin surar nan ta Al-Nahli.
Ana yi Liman kyakkyawan zato
Aliyu Abubakar Zazzau wani abokin Marigayin ne, wanda ya tabbatar da rasuwarsa a shafinsa. Zazzau ya ce Alaranman ya rasu ne ya limancin sallar dare. Amal Abubakar yake cewa ya samu labarin rasuwan malamin a cikin wannan wata mai alfarma. Amal ya ce irin wannan karshe na Sani Lawal abin madalla ne. A halin yanzu jama’a su na ta aika sakon ta’aziyyarsu ga ‘yanuwansa da dalibansa da daukacin mutanen Unguwar Samaru, tare da rokon samun irin cikawarsa. Watan Ramadan shi ne watan da ya fi kowane daraja da falala a addinin musulunci. Sannan kuma dare musamman irin na jiya yana daga cikin mafi daraja.